Isa ga babban shafi

Iraqi ta tono manyan kaburbura dauke da gawarwaki 605 da ISIS ta birne

Gwamnatin Iraqi ta sanar da cewa cikin shekaru 2 da suka gabata ta yi aikin kwashe gawarwakin mutane 605 da mayakan ISIS suka kashe tare da birne su a manyan kaburbura gab da babban gidan yarin da ke arewacin kasar.

Jami'an da suka gudanar da aikin tone kaburburan sun ce kaso mai yawa na gawarwakin sun dagargaje dalilin da ya sanya mika su ga sashen bincike don gano su.
Jami'an da suka gudanar da aikin tone kaburburan sun ce kaso mai yawa na gawarwakin sun dagargaje dalilin da ya sanya mika su ga sashen bincike don gano su. REUTERS/Stringer
Talla

Ma’aikatar da ke kula manyan kaburbura karkashin gwamnatin Iraqi da taimakon wata gidauniyar shahidai ne suka gudanar da aikin don sauya matsugunan mutanen da ta’addancin mayakan ISIS ya rutsa da su a Iraqi da Syria, lokacin da mayakan suka kwace iko da yankuna da dama na kasashen biyu cikin shekarar 2014.

A cewar bangarorin biyu tun a wancan lokaci mayakan ISIS sun rika dakko fursunoni daga gidan yarin da ke Badush a arewacin Iraqi suna yi musu kisan gilla tare da birnesu a manyan kaburbura.

A jawabinsa gaban manema labarai a birnin Baghdad, Dhiaa Karim shugaban sashen da ya jagoranci aikin bude kaburburan ya ce ya dauke tsawon shekaru 2 gabanin iya kamala bude kaburburan ko da ya ke sun yi nasarar dakko gawarwakin mutane 605.

A cewarsa sun samu cikakkun gangar jiki 204 sai kuma wasu sassa na jiki 401 sakamakon dadewarsu a birne kuma tuni suka mika su ga sashen bincike don gano ahalinsu inda tuni aka gano mutane 78.

A shekarar 2017 ne Iraqi ta sanar da nasarar murkushe barazanar ISIL sai dai tun bayan wannan lokaci ake ci gaba da gano manyan kaburburan da ‘yan ta’addan suka birne tarin mutanen da suka yiwa kisan gilla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.