Isa ga babban shafi

Pakistan za ta kori 'yan gudun hijirar Afghanistan miliyan 1 da dubu 300

Kungiyar Taliban ta yi kakkausar suka game da shirin gwamnatin Pakistan na tasa keyar dubban ‘yan Afghanistan zuwa gida, a bisa zargin wasunsu da hannu a hare-haren kunar bakin waken da aka rika kai wa a sassan kasar ta Pakistan, zargin da Taliban ke cewa babu gaskiya a cikinsa. 

Sansanin 'yan gudun hijirar Afghanistan da ke Pakistan.
Sansanin 'yan gudun hijirar Afghanistan da ke Pakistan. AFP - BANARAS KHAN
Talla

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce, yanzu haka akwai kimanin ‘yan Afghanistan miliyan 1 da dubu 300 da ke zaman gudun hijira a Pakistan, yayin da wasu karin dubu 880 ke da takardar izinin zama kamar kowa a sassan kasar. 

Sai dai a ranar Talatar da ta gabata, Ministan harkokin cikin gida Sarfraz Bugti, ya ce ‘yan Afghanistan miliyan 1 da dubu 700 suna zaune a Pakistan ne ba bisa ka’ida ba, dan haka ya basu nan da zuwa 1 ga  watan Nuwamba su fice daga  kasar, ko kuma a yi  amfani da karfi wajen mayar da su gida. 

A baya-bayan nan matsalolin tsaro sun fara ta'azzara a sassan Pakistan wanda ke da nasaba da hare-haren ta'addancin da suke ci gaba da tsananta, hare-haren da gwamnatin ta Pakistan ta alakanta da 'yan gudun hijirar na Afghanistan da galibinsu suka shafe tsawon shekaru a Islamabad.

Kwana guda bayan sanar da shirin na Pakistan ne, gwamnatin Afghanistan karkashin jagorancin Taliban, ta bayyana cewa sam 'yan gudun hijirar basu da alaka da matsalolin tsaron da Islamabad ke fuskanta kuma tilasta dawo da su gida a halin da ake ciki ba shi ne mafita ga bangarorin biyu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.