Isa ga babban shafi

Taliban ta sanar da kisan kwamandanta a Afghanistan

Kungiyar Taliban ta tabbatar da mutuwar guda cikin manyan kwamandojinta a Pakistan bayan da motar da ya ke ciki ta tarwatse lokacin da ya ke tsaka da tafiya a gabashin kasar Afghanistan jiya talata.

Wasu mayakan Taliban  a Pakistan.
Wasu mayakan Taliban a Pakistan. AP - Ishtiaq Mahsud
Talla

Reshen Taliban a Pakistan da aka fi sani da suna Tehreek-e-Taliban wato TTP, ta ce kwamandanta Abdul Wali da aka fi sani da suna Omar Khalid Khorasani, ya yi shahada sakamakon harin da makiya suka kai masa.

Wata majiya daga kungiyar ta TTP, ta ce sakamakon kisan da aka yi wa Abdul Wali, wasu kwamandojin kungiyar na barazanar kawo karshen mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninsu da gwamnatin Pakistan, sai dai ‘yan Taliban a cikin kasar da ke matsayin masu shiga tsakanin Pakistan da kungiyar na kokarin ganin ba a karya yarjejeniya.

Kwamandan na Taliban ya mutu ne tare da wasu baraden kungiyar uku da ke tare da shi a mota lokacin da harin ya faru a dai dai lokacin da su ke dawowa daga wani taron shugabannin kungiyar ta TTP.

A can baya dai mahukuntan Pakistan sun taba zargin makwabciyar kasar wato Afghanistan da yin amfani da jirage marasa matukar don kai hare-hare kan maboyar ‘yan Taliban da ke kusa da iyakokin kasashen biyu, to sai dai ba kasafai Afghanistan ke mayar da martani akan irin wadannan zargi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.