Isa ga babban shafi

Taliban ta haramta wa mata shiga jirgin sama

Kungiyar Taliban ta umarci kamfanonin jiragen saman Kasar Afghanistan da su dakatar  da yin bulaguro da matan da basa tare da muharramansu.

Wasu 'yan matan Afghanistan
Wasu 'yan matan Afghanistan AP - Rahmat Gul
Talla

A baya-bayan nan Taliban ta umarci jiragen saman Ariana Afghan hade da Kam Air haramta wa mata  yin bulaguro cikin jiragensu sai dai idan suna tare da  muharramansu.

Jami’an Ma’aikatar sufurin jiragen saman Kasar sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa kungiyar ta dauki matakin ne bayan kammala tattaunawa ta musamman cikin makon da ya gabata tsakanin wakilanta da hukumar shige da fice dake birnin kabul, da kuma hukumomin jiragen saman kasar.

Daukar matakin hana jiragen saman Afghanistan yin bulaguro da mata na daga cikin matakan da suka saba wa ka’idojin al’ummar kasar, wadda sabuwar gwamnatin ke yi tun bayan kwace mulki.

Ko a makon da ya gabata kungiyar ta haramtawa maza da mata ziyartar wuraren shakatawa lokaci guda, musamman wadanda ke babban birnin kasar.

Rufe makarantun mata, hana su ayyukan gwamnati, tare da tilasta musu sauya yanayin shigarsu, ya kasance tsatsaurar akida da Taliban ta dauka wajen tafiyar da Afghanistan, lamarin dake nuna sannu a hankali ana cigaba da ware mata a harkokin yau da kullum.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.