Isa ga babban shafi

An fara fito da mutanen da suka makale a cikin rami a kasar Indiya

Masu aikin ceto a India sun fara fitar da mutane 41 daga cikin ramin karkashin kasa da suka makale tsahon kwanaki 17 dai-dai lokacin da suke aiki. 

Yadda masu aikin ceto ke zakulo mutanen da ke karkashin kasa a Silkyara da ke arewacin India.
Yadda masu aikin ceto ke zakulo mutanen da ke karkashin kasa a Silkyara da ke arewacin India. © AP
Talla

 

Bayanai sun ce tuni aka fara aikin fitar da mutanen daga cikin ramin mai tsahon mita 90 daya bayan daya ta hanyar amfani da gadon marasa lafiya. 

Tawagar masu aikin ceton da ta kunshi mutane 4 har kaso uku sun fara aikin fitar da mutanen kamar yadda shugaban hukumar takaita afkuwar ibtila’I na kasar Syed Ata Hasnain ya shaidawa manema labarai. 

A cewar sa jami’an bada agaji sun dauki tsahon sa’o’I 400 suna aikin gano hanyoyin da ya kamata abi don shiga ramin mai matukar hadari, yana mai cewa za’a dauki minti uku zuwa biyar kafin ayi nasarar fitar da mutum guda cikin 41n da suka makale. 

Mutanen kananan ma’aikata sun makale a ramin mai tsahon kilomita 4 da rabi a karkashin kasar da ke jihar Uttarakhand guda daga cikin mafiya  talauci a kasar. 

Faya-fayan bidiyo sun nuna yadda mutanen ke cikin koshin lafiya,yayin da suke samun abinci, ruwa wuta da kuma tataciyyar iska har ma da magunguna da ake aike musu da sus ai dai kuma hanyar shiga ce aka rasa sai yau da suka shafe kwanaki 17. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.