Isa ga babban shafi

Dakarun Indiya sun ceto takwarorinsu a gabar tekun Somalia

Sojojin ruwa a India sun sanar da ceto illahirin takwarorinsu da ‘yan fashi suka yi yunkurin kai wa hari a cikin wani jirgin ruwa da ke yawo a tekun Arabia. 

Wani jirgin sojin ruwa na kasar Indiya
Wani jirgin sojin ruwa na kasar Indiya AFP - -
Talla

Wannan na zuwa ne bayan kiran neman agaji da dakarun suka yi, saidai duk da haka basu samu cafke ko daya daga cikin barayin ba. 

Sanarwar na cewa akalla mutane 21 aka ceto a babban jirgin dakon kaya kirar MV Lila Norfolk, kuma daga cikinsu akwai Indiyawa 15

Rundunar sojin ruwa ta kasar India ta ce dakarunta na gudanar da aikin sintiri ne a jirgin, lokacin da suka fuskanci barazanar kai musu hari a cikin tekun dake gabar ruwan Somalia, a arewacin Arabia. 

Kiran neman agajin gaggauwar da sojojin  su ka yi, ya yi sanadiyar tura jirgin yakin INS Chennai, da wani jirgin saman soji dan kai musu doki. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.