Isa ga babban shafi
Colombiya

Juan Manuel Santos ya lashe zaben kasar Colombia

TSOHON Ministan Tsaron kasar Colombia, Juan Manuel Santos, ya lashe zaben shugaban kasar, zagaye na biyu, bayan ya samu kusan kashi 70 na kuri’un da aka kada. Shidai Santos, dake samun goyan bayan shugaba mai baring ado, Alvaro Uribe, ya samu sama da kashi 48 na kuri’un, abinda ya bashi damar kada abokin takarar sa, kuma Tshohon magajin garin Bogota, Antanasa Mockus.Zababen shugaban, yayi alkawarin cigaba da aiyukan tsaron da shugaba Uribe ya tsaya akai, wajen magance matsalar kungiyar Yan Twayen Farc, inda ya shada msu cewa, lokaci yayi da zasu aje makamansu, domin ba zai sake tattaunawa da su ba.Santos ya kuma bukaci Yan tawayen da su sako mutanen da suke garkuwa da su, anna bada dadewa ba.Tun dai da Alvaro Uribe ya karbi ragamar tafi da kasar Colombia, a shekarar 2002, tashin hankali, garkuwa da jama’a da kuma hare haren bom, sun yi sauki a kasar.Wani kalubalen dake gaban shugaban, mai shekaru 58, shine batun rashin aikin yi, wanda ke addabar kasarr, da kuma tsadar kula da lafiyar iyali, a dai dai lokacin da ake fama da matsalar tattalin arzikin kasa.  

TSOHON Ministan Tsaron kasar Colombia, Juan Manuel Santos
TSOHON Ministan Tsaron kasar Colombia, Juan Manuel Santos REUTERS/John Vizcaino
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.