Isa ga babban shafi
MEXICO

Rundunar sojin Mexico ta gano gawawaki 72

RUNDUNAR Sojin kasar Mexico, tace ta bankado gawawkin wasu mutane 72 a wata gona, bayan fadar da akayi tsakanin jami’an tsaro, da masu safarar miyagun kwayoyi.Rundunar tace, an samu gawawkin ne a garin San Fernando, dake Jihar Tamaulipas, wanda ke iyaka da Jihar Texas, ta Amurka.Bayayanan da sojin sukayi dangane da harin, ya nuna cewar dakarun sama sun sanya hannu a ciki, kuma ya kaiga kama wani yaro, amma sauran Yan bindiga sun tsira da ransu.Sojin sun kwace bindigogi 21, harsasai sama da 6,600, da kuma motoci hudu.Akalla mutane 28,000 suka rasa rayukansu, a yakin da ake da masu safara miyagun kwayoyi a cikin kasar.  

Garin San Fernando
Garin San Fernando Photo: www.sanfernando.gob.mx
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.