Isa ga babban shafi
Kristmas

Yau Mabiya Addinin Krista ke Gudanar da bikin Kirsemeti

Yau Lahadi, mabiya addinin Krista ke gudanar da bikin Kirsemeti. A cikin sakonsa na bikin Shugaban Kiristoci mabiya Katolika Paparoma Benedict na XVI, ya nemi mabiya su yi amfani da wannan dama wajen tabbatar da zaman lafiya da kyautata zaman tare.Paparoma dake da shekaru 84 da haihuwa, ya nuna rashin jin dadi da yadda aka mayar da bukukuwan Kristimeti hanyoyin samun kudade tare da mantawa da hakikanin koyarwar.

Paparoma Benedict XVI
Paparoma Benedict XVI Reuters/Alessia Pierdomenico
Talla

Paparoma Benedict XVI ya gargadi masu kama karya da kuma masu haddasa fitina wajen tayar da zaune tsaye cewa Almasihu zai yi nasara akansu.

Ya nemi watsi da fankama da girman kai domin samun kusanta ga Ubangiji.

Dubban Kiristoci masu ziyarar ibada da Palesdinawa da suka hallara a garin Bethlehem mahaifar Annabi Isa, sun gudanar da addu’oin neman zaman lafiya wa duniya, albarkacin wannan rana ta Krismas.

Jami’an Palesdinawa dana Izira’ila sun bayyana cewa akwai kimanin baki dubu 50,000 dake halartar bikin na bana.

Anyi amfani da manyan na’urorin amsa kuwa inda ake gudanar da addu’oin cikin Larabci.

Garin na Bethlehem yana karkashin ikon Palesdinwa kuma babu nisa da birnin Kudus.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.