Isa ga babban shafi
EU-Amurka-Iran

Kasashen Turai da Amurka sun cim ma yarjejeniyar katse hulda da Iran.

Kungiyar kasashen Turai da gwamnatin kasar Amurka sun cim ma matsaya game da yarjejeniyar haramta shigo da danyen mai daga kasar Iran, Ministan harakokin wajen kasar Faransa ne ya bada sanarwar inda yace kafin karshen watan Janairu ne yazu yanke hukunci. 

Ministan harakokin wajen Faransa Alain Juppé a ganawar Ministocin kasashen Turai a  Lisbon.
Ministan harakokin wajen Faransa Alain Juppé a ganawar Ministocin kasashen Turai a Lisbon. REUTERS/Jose Manuel Ribeiro
Talla

Jakadun kasashen Turai sun ce akwai sauran aiki game da lamarin, kafin taron Ministocin waje na kungiyar, wanda za’a yi ranar 30 watan Janairu.

Ministan waje na kasar Faransa Allaine Jupe ya fadi cewa yana fatan taron da z’a gudanar zasu yanke shawara tare da daukar mataki game da harkar mai da kasar Iran.

Allain Jupre tare da takwaransa na Portugal, Paolo Portas ya fadawa taron manema labarai a Lisbon cewa suna ci gaba da dukkan kulle-kulle domin ganin sun cim ma burin su.

Wani jakadan ya tsegunta cewa an sami rarrabuwar kai game da katse mu’amulla da albarkatun man kasar Iran, amma daga bisani ra’ayi yazo daya, lokacin da kasar Girka da Spain da wasu kasashe da ke jikilar mai daga Iran suka amince.

A cikin shekarar 2010, kasashen Turai na jigilar Mai daga Iran da ya kai kusan kashi 6% na man da suke amfani da shi, domin kasar Iran ce ta 5 da ke aika masu da Mai, bayan kasar Rusha da Norway da Libya da Saudiyya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.