Iran ta bude hanyar tattaunawa da kasashen Yammaci
Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad yace gwamnatin shi, a shirye take domin hawa teburin sasantawa da manyan kasashen duniya, game da shirin Iran na kera makaman nukiliya bayan karfafawa kasar Takunkumi.
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Musuluncin Iran dai ta musanta zargin da kasashen ke yi game da shirinta na Nukiliya.
Kafafen yada labarun kasar, sun rawaito Shugaba Ahmedinejad na mayar da maratani kan kiran da hukumomin birnin Washington ke yi don sasantawa, inda yace babu bin da zai hana shi tattaunawa da kasashen yamma.
Taron farko da aka gudanar a bara domin warware rikicin Iran tsakanin kasashen Birtaniya da China da Faransa da Jamus da Rasha da Amurka an tashi ne baran-baram ba tare da sasantawa ba.
Shugabar harakokin kasashen wajen Kungiyar Tarayyar Turai, Catherine Ashton tace sun aika wa Iran da sako domin neman zama teburin sasantawa.
Sai dai har yanzu kasashen suna jiran amsar sakon da Ashton ta aika wa Iran a Watan Octoban bara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu