Republican: Romney ya lashe zaben fitar da gwani a Florida
Mitt Romney dan takarar shugaban kasar Amurka karkashin Tutar Jam’iyyar Republican ya lashe zaben zaben fitar da gwani a Jahar Florida, da kashi 46 na kuri’un da aka kada inda ya doke abokin karawarsa Newt Gingrich wanda ya zo na biyu da kashi 32.
Wallafawa ranar:
Bayan wannan nasara, Romney ya gargadi shugaba Barack Obama, cewar an zabe shi ne domin yin shugabanci, amma ya koma mabiyi, saboda haka lokaci yayi da zasu kawar da shi.
Nasarorin da Mitt Romney ya samu a Jahohin Carolina da Florida shi bayyana matsayinsa wanda zai kasance babban mai hamayya da Barack Obama a zaben shugaban kasa da za’a gudanar a watan Nuwamba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu