Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya yaba da kisan Osama da Ghaddafi

Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama, ya yaba da kawo karshen yakin Iraqi da kashe Osama bin Laden da Kanal Gaddafi, tare da bayyana wasu matakai da nasarorin gwamnatinsa a lokacin da ya ke jawabi a taron majalisar kasar.

Shugaban kasar Amurka  Barack Obama Lokacin da yake jawabi a gaban Majalisa
Shugaban kasar Amurka Barack Obama Lokacin da yake jawabi a gaban Majalisa
Talla

Wannan dai shi ne jawabin farko da Obama ya gabatar ga al’ummar Amurka domin kaddamar da yakin neman zabensa wa’adi na biyu a watan Nuwamba. Shugaban ya tabo batutuwa da dama amma ga wasu muhimmamai daga cikinsu:

Ingantaccen Tsarin tattalin arziki.

Mista Obama ya jaddada muhimmacin inganta tattalin arzikin Amurka da zai kasance cikin sauki ga kowa a kasar tare da sake bayyana matsayin shi game tsarin haraji ga Attajiran Amurka matakin da Jam’iyyar adawa ta Republican ke adawa da shi.

A cewar Obama ya zama wajibi Amurka ta sauya tsarin harajinta domin attajirai kamar shugaban kasa da sauran ‘Yan majalisu zasu biyan harajin  da ya dace.

Bisa tsarin harajin dai idan mutum yana samun kudi dala Miliyan $1 a shekara, zai biya kudin haraji kashi 30 cikin 100 na kudaden da ya ke samu.

Sai dai Obama yace babu wani karin harajin ga mutanen da ke samun kudi kasa da $250,000 a shekara.

Inganta Masana’antu

Mista Obama ya bayyana kudirin sauya tattalin arzikin Amurka wajen inganta masana’antun kasar bayan kwashe shekaru ana fama da matsalar aikin yi sabanin kasar China. tare da alkawalin inganta tattalin arziki domin kafada da kafada da kasar China.

Babban Kwamanda

Shugaba Obama ya yaba da kisan Shugaban Alka’ida Osama Bin Laden da Kanal Gaddafi tsohon shugaban kasar Libya.

Obama kuma yace a karon farko babu wani Ba’amurke da ke yaki a kasar Iraqi bayan kwashe tsawon shekaru Amurka na yaki a kasar. Shugaban  yace tsawon shekaru 20 da suka gabata, Al'ummar Amurka basu cikin fargabar Osama kuma yanzu haka manyan kwamandojin kungiyar alka’ida, Amurka tafi karfinsu. A cewar Obama dakarun Amurka sun fara dawowa gida.

Sasantawa da Iran

Mista Obama yace akwai yiyuwar sansantawa da kasar Iran game da rikicinta da Amurka da sauran kasashen yammaci akan shirinta na inganta makamashin Nukiliya.

wannan jawabin na shugaban wata fargaba ce da yake nunawa bayan da kasar Iran ta yi barazanar rufe mashigin ruwan Hormuz hanyar da ake fataucin mai zuwa kasashen duniya.

Sai dai Obama yace Amurka zata yi kokarin haramtawa iran inganta shirinta na Nukiliya ta hanyar sasantawa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.