Isa ga babban shafi
Birtaniya-Somalia

Taron kasashen Duniya a Birtaniya game da Somalia

Wakilan gwamnatocin kasashen duniya zasu gudanar da taro a birnin Landon, a wani sabon yunkuri domin gano mafita daga rikicin kasar Somaliya da Fashin jirgin ruwa da kuma yadda za’a magance Talauci da ya addabi kasar da wasu kasashen Afrika.

Sansanin 'Yan gudun hijira a kasar Somalia
Sansanin 'Yan gudun hijira a kasar Somalia UN Photo/Stuart Price
Talla

Taron na zuwa bayan gwamnatin Somalia ta bayyana samun nasara a yakinta da kungiyar Al Shabeb, kuma Taron zai kunshi wakilan kasashe 50 da hukumomi, da zasu hada da Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton, da Sakataren Majalisar Dinkin duniya Ban Ki-moon.

Sai dai kasashen zasu yi kokarin mayar da hankali wajen samar da hanyoyin magance matsalar yunwa da ke barazana ga wasu kasashen Afrika musamman Somalia.

Gwamnatin Birtaniya tace babban muradin ta shi ne samar da zaman lafiya da tsaro mai dorewa a Somalia da ke barazana ga kasar.

A dai dai karfe 10:00 na safe agogon GMT Fira Ministan Birtaniya David Cameron, zai bude taron da jawabinsa a gaban mahalarta.

Sauran mahalarta Taron sun kunshi wakilan kasashen Larabawa da kungiyar Tarayyar Turai da Afrika da shugaban kasar Somalia.

Tsawon shekaru 20 kasar Somalia ke fama da tashe-tashen hankula, kuma tun a shekarar 1999 babu wata tsayayyar gwamnati a kasar inda kungiyar Al Shebab da sauran kungiyoyin ‘Yan Tawaye suka karbe ikon wasu yankunan kasar.

Sai dai a ranar Laraba ne Fira Ministan Somalia Abdiweli Mohamed Ali ya bayyana cewa sun karbe ikon kudu maso yammacin Baidoa yankin da ke karkashin kungiyar Al Shebab.

A makon jiya ne kwamandan Al Qaeda Ayman al-Zawahiri ya fitar da sanarwa cewa sun kulla kawance da Al shebab.

Akwai dai matsaloli da suka shafi fashin jirgin ruwa da matsalar yunwa da ake fama da su a kasar Somalia.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.