Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Mutane 8000 suka mutu a Syria, inji MDD

Majalisar Dinkin Duniya tace Fiye da mutane 8000 ne sun hallaka a rikicin kasar Syria wanda aka kwashe tsawon shekara ana gudanarwa domin adawa da gwamnatin Bashar Al Assad. Nasir Abdullaziz shugaban babban zauren majalisar, yace akasarin wadanda suka mutu mata ne da kananan yara .

Hotunan gawawwakin wadanda suka mutu a rikicin kasar Syria.
Hotunan gawawwakin wadanda suka mutu a rikicin kasar Syria. REUTERS
Talla

Wannan kalaman suna zuwa ne bayan ficewar Kofi Annan daga Syria manzon na musamman da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Larabawa suka aika domin sasanta rikicin kasar wanda ya gana da Shugaba Bashar al-Assad kuma yanzu haka yana kasar Turkiya domin ganawa da ‘yan adawa.

Sai dai gwamnatin kasar Syria bata gasgata wannan rehoton na Majalisar Dinkin Duniya ba.

Bayan ganawar Mista Annan da Fira Ministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan a Ankara, Mista Annan ya amsa cewa akwai lokaci mai tsawo da za’a kwashe kafin a shawo kan rikicin kasar Syria.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.