Brazil da Amurka zasu inganta huldar kasuwanci
Shugaban kasar Vrazil Dilma rousseff zata kai ziyarar farko zuwa kasar Amurka domin tattauna bututuwan da suka shafi inganta huldar kasuwanci da ilimi da huldar Diflomasiya.
Wallafawa ranar:
Kasar Brazil ita ce kasa ta shida a habakar tattalin arzikin duniya, kuma kasa ta Takwas da ke huldar kasuwanci da kasar Amurka.
Amma kasar Brazil tana neman goyon bayan Amurka ne a kudirinta na neman kujerar din-din a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.
A yau Litinin ne ake sa ran shugaba Rousseff zata gana da Shugaban kasar Amurka Barack Obama a fadar White house.
Ana sa ran ganawar shugabannin biyu zasu mayar da hankali wajen inganta huldar kasuwancinsu da ci gaban ilimi tsakanin kasashen biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu