Venezuela
Chavez zai shiga zabe karo na uku a Venezuela
Shugaban Kasar Venezuela, Hugo Chavez mai fama da rashin lafiya, ya yi rajistar takarar shugabancin kasa, a karo na uku, a zaben da za’a gudanar a watan Octoba mai zuwa bayan kwashe lokaci shugaban yana jinya.
Wallafawa ranar:
Talla
Shugaba Chavez ya shiga cikin tawagar dubban magoya bayansa a Caracas, bayan yin rajista a ofishin hukumar zabe, inda ya yi rawa da waka don tabbatar wa magoya bayansa yana cikin koshin lafiya.
Shugaban ya bayyana shekarar bana a matsayin mafi wahala a gare shi, amma kuma ya godewa Ubangiji.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu