Venezuela
Venezuela zata baiwa Syria Man Fetur
KasarVenezuela t ace zata tura jirgin ruwa dauke man fetur zuwa Syria, wanda shine na uku da kasar ke baiwa gwamnatin Syria mai fama da tashe tashen hankula a gida.
Wallafawa ranar:
Talla
Matakin na kasar Venezuela wani koma baya ne ga kasahsen Yammacin duniya, wadanda suka sanyawa Syria takunkumi. Shugaban Syria Bashar al-Assad yana fuskantar bore na fiye da shekara guda, tare da takunkumi daga kasashen Duniya, wadanda ke neman ganin gwamntin kasar ta kawo karshen tsauraran matakan da take dauka kan masu zanga zanga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu