Isa ga babban shafi
Myanmar-Faransa

Ziyarar Suu Kyi a Faransa

Shugabar adawar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi zata kai ziyarar kwanaki uku a kasar faransa, inda ake saran zata gana da shugaba Francois Hollande tare da neman goyon bayan kungiyoyin kare hakkin bil’adama don ci gaban Demokradiyya a kasarta.

Aung San Suu Kyi Shugabar adawar kasar Myanmar
Aung San Suu Kyi Shugabar adawar kasar Myanmar Reuters
Talla

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Myanmar, Bernard Valero, yace Suu kyi zata isa birnin Paris ta hanyar jirgin kasa daga London, inda ake sa ran zata gana da Ministan harkokin waje, da kuma shugabanin Majalisun Faransa.

Suu Kyi mai shekaru 67 ta kwashe kwanki tana Ziyara a kasashen Turai da suka hada da Switzerland da Ireland da Norway da Birtaniya kafin tai so Faransa.

A ranar 13 ga watan Yuni ne Suu Kyi ta kaddamar da ziyara a kasashen Turai yankin da ta yi karatu a shekarun baya kafin ta koma fafutikar Siyasa a kasar Myanmar.

Sai dai Ziyarar Suu Kyi na zuwa ne a dai dai lokacin da rikicin ke ci gaba da aukuwa a sassan yankuna Myanmar inda mutane da dama suka yi gudun hijira saboda rikicin addini tsakanin mabiya Buddhist da Musulmin Rohingya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.