Isa ga babban shafi
Kenya

Hadarin jirgi ya kashe ‘Yan kasar Jamus Biyu da matukan jirgi a Kenya.

Wasu ‘Yan yawan bude ido su biyu daga kasar Jamus da wasu matuka jirgin sama suma su biyu ne su ka rasa rayukansu a wani hadarin jirgin sama da ya auku a kasar Kenya.Jirgin dai ya fado ne a cikin wani dandalin namun daji da ake kira Maasai Mara National Park, ya kuma raunata wasu ‘Yan yawan bude ido uku a wurin day a fadi. 

Wani jirgin sama da ya taba faduwa a wani tsbirin kasar Kenya
Wani jirgin sama da ya taba faduwa a wani tsbirin kasar Kenya REUTERS/Peter Greste
Talla

A cewar babban Dan sandan yankin, Peterson Maelo, mutane hudu a take su ka mutu.

Bincike ya kuma nuna cewa, jirgin na dauke ne da ‘Yan kasar Jamus su biyar da Amurkawa hudu da kuma wasu ‘Yan kasar Czech su biyu.

Sai dai binciken kamar yadda Kamfanin Dillancin labaran AFP ya rawaito ya nuna cewa ba a san ko su waye matukan jirgin ba.

Wani ma’aikacin gandun namun dajin, Michael Koikai, ya ce jirgin ya fado ne jim kadan bayan ya tashi sama daga dan karamin filin saukar jirgin Ngerende.

‘Yan yawan bude da dama sukan gwammace su hau jirgi su isa masaukinsu a maimakon tafiya ta hanyar mota wacce ke da wahala da kuma rashin kyan hanya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.