Jam’iyyar Republican ta tsayar da Romney a matsayin Dan takara
Jam’iyyar adawa ta Republican a Amurka ta tsayar da Mitt Romney a matsayin dan takarta wanda zai kara da Shugaba Barrack Obama a zaben shugaban kasa da za’a gudanar a watan Nuwamba. Ann Uwargidan Romney tace Mijinta ba zai ba Jam’iyyar Republican kunya ba.
Wallafawa ranar:
Mitt Romney shi ne dan takarar da ya samu rinjayen kuri’u Bayan kammala zaben fitar da gwani a Jahohin Amurka, Romney ya samu adadin kuri’un da ake bukata kafin tsayar da Dan takara domin ya samu goyon bayan wakilan Jam’iyyar 1,144.
Romney mai shekaru 65 na haihuwa kuma attajirin dan kasuwa, a gobe Alhamis ne zai gabatar da jawabin amincewa da jagorantar Jam’iyyar Republican a zaben shugaban kasa a Tampa Jahar Florida.
Wani sakamakon zaben jin ra’ayin jama’a da aka gudanar ya nuna Romney yana kafada da kafada ne da Obama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu