Isa ga babban shafi
Venezuela

Shugaba Chavez ya sake lashe zaben Venezuela

Huhkumar Zaben Kasar Venezuela, ta bayyana shugaba Hugo Chavez, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar, dan samun wa’adi na uku, inda ya samu sama da kashi 54 na kuri’un da aka kirga, yayin da Dan takaran Yan adawa, Henrique Capriles, ya samu kashi sama da 44.Tuni Capriles ya amsa shan kaye ya kuma taya shugaba Chaves murnar nasarar da ya samu.Tuni dai bukuwa suka barke a birnin Caracas, bayan da shugaban hukumar zabe, Tibisay Lucena ta sanar da sakamakon zaben, wanda ya baiwa shugaba Hugo Chaves nasara, a karo na uku.Lucena tace shugaba Chavez ya samu kuri’u 7,444,082 yayin da Capriles ya samu kuri’u 6,151,554 daga cikin kuri’u miliyan 19 na al’ummar kasar.An yi ta gudanar da wasan wuta, dan bayyana farin ciki, yayin da zababen shugaban kasar, ya bayyana farin cikin sa ta yanar gizo, yana cewa, nagode jama’a ta, Allah Ya taimaki Venezuela, Nagode Allah, na kuma gode muku.Daruruwan magoya bayan shugaban sun cigaba da gudanar da bukukuwa a gaban fadar shugaban kasar dake Miraflores, kafin ma a sanar da sakamakon, inda ake ta kade kade da raye raye.Yayin da yake jawabi a Cibiyar yakin neman zaben sa, Capriles yace a matsayin sa na wanda ya san demokradiya, ya amsa shan kaye, kuma yana taya shugaba Chaves murna, domin shi ba zai ja da abinda al’ummar Venezuela suka zabarwa kansu ba.Dan takaran yace, a matsayin sa na wanda ya amince da demokradiya, ya dace ya san yadda zai samu nasara, da kuma yadda ba zai samu ba. 

Shugaban kasar Venuzuela Hugo Chávez,
Shugaban kasar Venuzuela Hugo Chávez, REUTERS/Tomas Bravo
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.