Isa ga babban shafi
Lebanon-Amurka

Amurka za ta taimaka wa Lebanon gano wadanda suka kai harin Bom

Gwamnatin kasar Amurka tace zata taimakawa kasar Lebenon gudanar da bincike domin gano wadanda suka kai harin Bom day a sanadiyar mutuwar wasu manyan Jami’an tsaron kasar, kamar yadda Hillary Clinton da Firaministan Lebanon Najib Mikati suka amince a tattaunawarsu ta wayar Salula.

Masu zanga-zanga a kasar Lebanon a lokacin da suke arangama da 'Yan Sanda bayan kai harin Bom da ya yi sanadiyar mutuwar Jami'an tsaron kasar
Masu zanga-zanga a kasar Lebanon a lokacin da suke arangama da 'Yan Sanda bayan kai harin Bom da ya yi sanadiyar mutuwar Jami'an tsaron kasar REUTERS/Ahmed Jadallah
Talla

A ranar jumu’a ne aka kai harin Bom da ya yi sanadiyar mutuwar Wissam al-Hassan da wasu mutane biyu.

Bayan kai harin kuma an samu arangama tsakanin ‘Yan Sanda da masu zanga zanga, a birnin Beirut, yayin da masu zanga zangar suka yi yunkurin abkawa ofishin Firaministan kasar, Rajib Mikati, wanda suke bukatar ganin ya yi murabus, sakamakon yadda aka kashe babban jami’in tsaro, Hassan Wissam.

Daruruwan Masu zanga zangar, da ke dawowa daga jana’izar Janar Wissam Hassan, sun yi zargi hukumomin kasar Syria da kitsa harin da aka sa a motar da ya yi sanadiyyar kashe mutane Takwas, tare da raunata wasu 126.

Mista Hassan mai shekaru 47 yana cikin masu adawa da Hariri kuma masu adawa da gwamnatin Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.