Isa ga babban shafi
MDD

Larabawa Kusan rabin Miliyan ke dauke da Cutar Kanjamau, inji MDD

Wani Rahoton Majalisar Dinkin Duniya yace mutane kusan Rabin Miliyan a kasashen Larabawa suna dauke da cutar Kanjamau ko Sida a shekaru Takwas da suka gabata zuwa 2009.

Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya a Genève,
Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya a Genève, www.unaids.org
Talla

Inji Rahoton na hukumar kula da cigaban kasa-da-kasa ta Majalisar dunkin Duniya, adadin yawan matasa, da kananan yara da ke dauke da cutar kanjamau a kasashen Larabawa, ya ninka daga dubu 180 zuwa dubu 470.

Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar da wannan rahoton ne a wani taron da aka gudanar a Riyadh, kan batun shawo kan cutar Kanjamau da kungiyar kasashen Larabawa da Saudi Arebiya suka shirya.

Haka ma yawan wadanda suka mutu sakamakon cutar ya haura daga Dubu Tamanin a shekarar 2001 zuwa Dubu Ashirin a shekarar 2009.

A kasashen Djibouti da Somaliya, akalla kashi 2.5 ne ke dauke da wannan cutar, abinda ya daga hankalin jama’a, da bukatar a dauki matakin gaggawa

Sai dai a dukkanin fadin Duniya, an samu raguwar kamuwa da cutar da akalla kashi 2.5 a shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.