Isa ga babban shafi
Lafiya

Kasar Norway ne iyaye mata suka fi shan dadi amma a Nijar suka fi shan wahala

A wani sabon Rahoto game da halin rayuwar iyaye mata da hukumar kare lafiyar kananan yara ta fitar, ya nuna Nijar ce kasar da iyaye Mata ke shan wahala bayan maye gurbin kasar Afghanistan a karon farko. Kasar Norway ce a matsayin kasa ta farko da iyaye Mata ke shan dadi a jerin kasashe 165 da aka kwatanta rayuwarsu.

Matan kasar Afghanistan a lokacin gudanar da bukin ranar mata a yankin Ghazni a ranar 8 ga watan Maris
Matan kasar Afghanistan a lokacin gudanar da bukin ranar mata a yankin Ghazni a ranar 8 ga watan Maris REUTERS/Mustafa Andaleb
Talla

Hukumar kare kananan yara "Save The children" ta yi la’akari ne da matsalolin da suka shafi kiwon Lafiya da karancin Ilimi da rashin samun abinci mai gina jiki da kuma tattalin arziki.

Hukumar tace matsalar karancin Abinci da ke addabar yankin Sahel ita ce ke barazana ga rayuwar Miliyoyan kananan yara a yankin.

Sai dai kasar Amurka ta sake harba wa sama daga matsayi na 31 a bara kuma ta fado karkashin manyan kasashen Duniya masu karfin tattalin arziki.

A cewar Shugaban hukumar Carolyn Miles, Mata a kasar Amurka na iya mutuwa wajen haihuwa sau bakwai tsakanin matan da ke kasashen Italiya da Ireland.

A taron kasashe Takwas masu karfin tattalin arzikin duniya na G8 ana sa ran shugaba Obama zai tabo batun inganta samar da abinci da ayyukan noma.

Rehoton hukumar Save the children yace rashin samun abinci mai gina jiki shi ne ke haifar da yawan samun mace macen mata da kananan yara a wajen haihuwa.

Hukumar ta yi gargadin cewa idan uwa bata da isassar lafiya da rashin wadataccen ilimi tare da yin ayyukan wahala zai hana ta shayar da Jariri yanda ya dace.

Hukumar tace hanya mafi sauki ta magance matsalar rashin Abinci mai gina jiki tsakanin Uwa da jaririnta ita ce kula da kwanaki 1,000 na farko tun daga samun ciki.

Hukumar ta yi kira ga shugabannin duniya domin gaggauta daukar mataki wajen magance matsalar yawan mace macen mata da rashin abinci mai gina jiki a taron kasashen G8 da za’a gudanar nan da makwanni biyu.

Kasar Guinea Bissau da Mali da ke fuskantar rikicin siyasa sune a matsayin kasashe na hudu dana Biyar da rayuwar mata ke cikin mawuyacin hali bayan Afghanistan a matsayi na Biyu sai kasar Yemen a matsayi na uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.