Isa ga babban shafi
NATO-Turkiya-Syria

NATO za ta kare Turkiya daga hare haren Syria

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO/OTAN za ta amince da matakin taimakawa kasar Turkiya na girke garkuwar harbo duk wani makami da kan iya fitowa daga Syria. Ministocin harkokin wajen kasashen NATO 28, za su gudanar da taronsu a Brussels domin amincewa da bukatar Turkiya.

Tawagar dakarun Turkiya akan hanyarsu zuwa kan iyaka da Syria, kusa da birnin Kilis
Tawagar dakarun Turkiya akan hanyarsu zuwa kan iyaka da Syria, kusa da birnin Kilis Reuters/
Talla

Gwamnatin Turkiya ce dai ta nemi taimakon daga NATO domin kare kan iyakokinta da Syria.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ke cewa, girke makamin zai iya kara tankiyar da ke tsakanin kasashen Biyu.

Amma Sakatare Janar na kungiyar NATO, Anders Fogh Rasmussen ya bayyana shirin amincewa da girke makamin, yana mai cewa bukatar NATO shi ne kare kawayenta.

Tuni dai Shugaban Amurka Barack Obama ya gargadi Bashar al Assad cewar zai fuskanci barazana idan har ya fara amfani da makamai masu guba ga Jama’ar shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.