Isa ga babban shafi
kasashen Larabawa

Shekaru Biyu ke nan ana zanga-zanga a kasashen Larabawa

Shugabannin Kasashen Larabwa da dama ne suka fuskanci zanga-zangar adawa da su tun a watan Disembar shekarar 2010 wanda ya kawo karshen faduwar Gwamnati a Tunisia da Masar da Libya. Irin wannan zanga-zangar ce ke ci gaba da kadawa a kasar Syria bayan ta lafa a kasashen Bahrain da Yemen.

Daruruwan Magoya bayan Mohammed  Morsi na Masar
Daruruwan Magoya bayan Mohammed Morsi na Masar REUTERS/Asmaa Waguih
Talla

TUNISIA

Sabuwar Zanga-zangar kin jinin Gwamnatin kasashen Larabawa ta samo Asali ne daga Tunisia a shekarar 2010 inda a tsakiyar birnin Sidi Bouzid, wani matashi mai sayar da kayan marmari ya haifar da zanga-zangar da ta bazu zuwa sassan kasashen Larabawa.

A ranar 14 ga watan Janairun shekarar 2011 masu zanga-zanga suka hambarar da gwamnatin Zine El Abidine Ben Ali wanda yanzu haka ya samu mafaka a Saudiya bayan kwashe shekaru 23 yana shugabancin kasar Tunisia.

A watan Oktoba ne kuma Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta samu nasarar lashe zaben ‘Yan majalisu.

Amma har yanzu akwai ‘yan kasar Tunisia da ke ficewa daga kasar saboda rashin samun biyan bukatun abinda suke nema bayan hambarar da gwamnatin Ben Ali.

MASAR

A watan Yunin shekarar 2012 aka bayyana sunan Mohammed Morsi na Jam’iyyar Brotherhood a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Masar da rinjayen Kuri’u kashi 51.73 bayan kwashe lokaci al’ummar kasar suna gudanar zanga-zangar da ta yi awon gaba da Hosni Mubarak wanda ya kwashe tsawon shekaru 30 yana shugabancin Masar.

Morsi shi ne shugaba na Farko daga bangaren Jam’iyar ‘Yan Uwa Musulmi.

Sai dai bayan Zaben shi wani sabon Rikici ya sake kunno kai bayan shugaban ya karawa kansa karfin fada aji a cikin kasar a ranar 22 ga watan Nuwamba.

Yanzu haka akwai dimbin masu adawa da Gwamnatin Morsi wanda ya nemi al’ummar kasar su jefa kuri’ar zaben raba gardama don yi wa kundin tsarin mulkin kasar Kwaskwarima.

LIBYA

A ranar 20 ga watan Oktoban shekarar 2011 ‘Yan tawayen Libya suka kashe Kanal Gaddafi bayan sun karbe ikon birnin Tripoli tare da taimakon kungiyar kwancen tsaro ta NATO/OTAN. Rahotanni sun ce Akalla mutane 30,000 suka mutu sakamakon yakin da aka gwabza tsakanin dakarun Gaddafi da ‘Yan tawaye.

Tutar Kasar Libya
Tutar Kasar Libya

Gaddafi ya kwashe tsawon shekaru sama da 40 yana shugabanci a Libya.

A watan Nuwamban shekarar 2012 aka rantsar da Sabuwar Gwamnatin Libya karkashin jagorancin Firaminista Ali Zeidan.

Amma har yanzu kasar Libya na fama da hare hare daga magoya bayan tsohon shugaba Kanal Gaddafi da kuma wasu ‘Yan tawaye da aka saba masu bayan faduwar gwamnati.

SYRIA

A ranar 15 ga watan Maris shekarar 2011 aka fara rikicin Syria tsakanin Gwamnatin Bashar Assad da masu adawa da shi.

Rikicin wanda aka kwashe tsawon watanni 21 ya lakume rayukan mutane sama da 42,000 yawancinsu fararen hula.

Ministan harakokin wajen Rasha Mikhail Bogdanov yace gwamnatin Bashar Assad na kan hanyar rugejewa saboda goyon bayan da ‘Yan tawaye ke samu daga kasashen Yammaci da sauran Mayaka a yankin Gabas ta tsakiya.

YEMEN

A watan Fabrairun shekarar 2012 ne Shugaban Yemen Ali Abdullah Saleh ya mika mulki ga mataimakinsa Abdrabuh Mansur Hadi bayan kwashe tsawon watanni 10 Al’ummar kasar na zanga-zangar adawa da mulkin shekaru 33  da ya kwashe yana yi a Yemen.

Kafin mika mulki dai Ali Abdallah Saleh ya nemi kariya daga duk wata Tuhuma bayan mutuwar daruruwan mutane a zanga-zangar adawa da shi.

A lokacin zanga-zangar ne dai kungiyar Al Qaeda ta samu nasarar karbe ikon yankunan kudanci da gabacin kasar.

BAHRAIN

A kasar Bahrain Mabiya Akidar Shi’a ne suka haifar da zanga-zanga suna neman a samar da kundin tsarin mulki amma zanga-zangar ba ta yi tasiri ba domin a watan Maris ne Dakarun kasar karkashin jagorancin mabiya Sunni suka taka masu burki.

JORDAN

A ranar 14 ga watan Janairun shekarar 2011 zanga-zanga ta barke a kasar Jordan inda al’ummar kasar suka bukaci samar da sauye sauyen siyasa da tattalin arziki amma zanga-zangar ba ta yi tasiri ba kamar sauran kasashen Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.