Isa ga babban shafi
Venezuela

Rashin lafiyar Chavez na Venezuela ta yi tsanani

Rahotanni Daga kasar Cuba, sun nuna cewar shugaba Hugo Chavez na Venezuela, na fama da cutar huhu da ke shafar numfashinsa bayan yi masa Tiyata, abinda ya sa manyan jami’an Gwamnatin kasar suka gudanar da wani taron gaggawa.

Shugaban kasar Venezuela, Hugo Chavez
Shugaban kasar Venezuela, Hugo Chavez
Talla

Chavez mai shekaru 58 na haihuwa, karo hudu ken an ana masa Tiyatar cutar Sankara a kasar Cuba.

Wata Sanarwa da ta fito daga Ministan yada labaran kasar Venezuela, Ernesto Villegas yace matsalar yanzu ta shafi numfashi.

Jami’an gwamnati kasar sun bayyana shakkun game da rashin lafiyar Chavez da suka ce ta yi tsanani domin har yanzu babu tabbas akan ko zai iya ci gaba da mulkin kasar.

A ranar Bakwai ga watan Oktoba ne aka sake zaben Hugo chavez a matsayin shugaban kasa amma yanzu yana fuskantar kalubale daga ‘Yan adawa saboda rashin lafiyar shi.

Dama dai kundin tsarin mulkin kasar ya bukaci a gudanar da sabon zabe cikin kwaki 30 idan shugaban kasa bai iya karban Rantsuwar kama aiki ba.

Tuni dai Chavez ya zabi Maduro a matsayin mukaddashinsa kafin ya je neman magani a Cuba ba tare da mika masa mulki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.