Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya zargi Republican da yin zagon kasa akan kudirin zabtare kudaden Gwamnati

Shugaban Amurka Barack Obama ya zargi Jam’iyyar Adawa ta Republican da yin zagon kasa ga kudirin gwamnatin shi na kokarin cim ma matakin zabtare kudaden da gwamnati ke kashewa wanda zai fara aiki a ranar Juma'a.

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Larry Downing
Talla

Akwai sabani da aka samu tsakanin ‘Yan Jam’iyyar Democrat da ‘yayan Jam’iyyar Republican wadanda suke zargin juna tare cacar baki a zauren majalisa game da kudirin.

Kudaden da Gwamnatin Obama ke shirin zabtarewa sun kai sama da Dala Miliyan Dubu Tamanin domin farfado da tattalin arzikin kasar.

Ana saran Obama zai ciwo kan ‘yayan Jam’iyyar Republican a fadar White House inda zai gana da kakakin Majalisa John Boehner da babban Senatan Jam'iyyar Mitch McConnell don cim ma kudirin.

Jam’iyyar Democarat tana kokarin tursasawa Jam’iyyar adawa ta Republican amincewa da kudirin samun kudaden shiga ta hanyar haraji daga Attajiran Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.