Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Paparoma Francis zai halarci bukukuwan ranar matasa ta duniya a Brazil

Sabon shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Francis na daya, ya ce zai halarci bukukuwan zagayowar ranar matasa ta duniya da za a gudanar a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil a cikin watan Yulin wannan shekara.

Paparoma Francis
Paparoma Francis REUTERS/Paul Hanna
Talla

Paparoma, wanda ke gabatar da jawabi a gaban magoya bayan darikar Katolika da ke halartar addu’o’in ranar yau lahadi, ya ce shi da kuma sauran mukarrabansa, da yardar Allah za su kasance tare da sauran matasa a wadannan bukukuwa na bana.
A ranar larabar da ta gabata shugabar kasar ta Brazil Dilma Roussef ta bayyana cewa tuni sabon shugaban na mabiya darikar Katolika ya tabbatar da cewa zai halarci bukukuwan na ranar matasa. Yayin da wasu rahotanni ke cewa tun kafin zuwa sabon Paparoman ne wanda ya gabace shi wato Bennedict na 16, ya soma nuna alamun cewa Vatican tana daukar wadannan bukukuwa da za a gudanar a Brazil da matukar muhimmanci

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.