Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Shugabannin Katolika sun shiga fadar Vatican domin zaben sabon Fafaroma

Shugabannin mabiya Darikar Katolika kimanin 115 sun hallara Birnin Rome domin zaben sabon Fafaroma, bayan Fafaroma Benedict na Sha Shida ya yi murabus. Shugabannin da a ke kira Cardinals sun ce za su gana da juna kafin su fara muhawara game da zaben sabon Fafaroman a dakin taro na Sistine Chapel.

Shugaban Darikar Katolika na Amurka Francis George, da na India Telesphore Toppo da kuma shugaban Katolika na Najeriya John Olorunfemi Onaiyekan
Shugaban Darikar Katolika na Amurka Francis George, da na India Telesphore Toppo da kuma shugaban Katolika na Najeriya John Olorunfemi Onaiyekan REUTERS/Max Rossi
Talla

Shugabannin za su kada kuri’a sau hudu a rana har sai kashi biyu cikin uku sun amince da sabon Fararoma.

Akwai Babban kalubalaen da Cocin katolika ke fuskanta da suka hada da matsalar fyade da cin hanci da rashawa, lamarin da rahotanni suka ce sun fi karfin Fafaroma Benedict mai shekaru 85 na haihuwa.

Duk wanda zai gaji Benedict sai ya yi kokarin yaki da wadannan matsalolin a fadar Vatican.

Akwai sunayen jagororin darikar daban-daban da aka gabatar daga yankunan kasashen Duniya da suka cancanci a zabe su a matsayin Fafaroma, wadanda kuma dukkaninsu ke shaukin jagorantar mabiyar darikar ta Katolika.

Daga ranar Laraba, ana bukatar kada kuri’a guda biyu da safe da kuma yammaci, za’a kona kuri’a idan an kammala zaman kada kuri’ar kafin a samu dan takara wanda ya samu rinjayen kuri’u.

Idan dai aka ga fitowar hayaki daga dakin zaman shugabannin a fadar Vatican, ya nuna an zabi sabon Fafaroma na 266.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.