Isa ga babban shafi
Amurka-Marathon

An cafke mutum na biyu da ake zargi da hannun a harin Boston

An kwantar da mutum na 2 da ake zargi da kai harin Bam a birnin Boston na kasar Amurka a asibiti cikin mawuyacin hali, bayan da aka kama shi a tsakanin daren jiya juma’a zuwa safiyar yau asabar, kamar yadda hukumar ‘yan sandan Massachusetts ta sanar.

Mutane biyu da ake zargin cewa sun kai harin Boston
Mutane biyu da ake zargin cewa sun kai harin Boston Reuters
Talla

Matashin mai suna Dshokar Tsaraev ya boye ne a cikin wani jirgin ruwa wanda aka ajiye a bayan wani gida a Watertown da ke wajen birnin na Boston, kuma yan sanda sun yi nasarar gano maboyarsa ne tare da taimakon wani mazauni unguwar da ya shaida digar jinni har zuwa cikin kwale-kwalen.

Dan uwansa na jinni mai suna Tamerlan, da shi ma aka zarga da kai harin na Boston da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3 tare da jikkata wasu sama da 100, ‘yan sanda sun kashe shi a cikin daren alhamis zuwa wayewar safiyar jiya juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.