Isa ga babban shafi
Amurka

Mahaifiyar michael Jackson na zargin an hallaka dan nata ne

Mahaifiyar Michael Jackson, wato Katherine Jackson na zargin kanfanin da ke tallata Dan nata da hadin baki wajen kashe shi, wajen bashi magunguna da suka yi sanadiyar mutuwar mawakin.Mahaifiyar Jackson tace kanfanin ne ke da alhakin mutuwar Dan nata.Sai dai lauyan kanfanin, Marvin Putnam ya musanta zargin, inda yake cewa Michael Jackson yayi rufa rufa kan halin lafiyar sa da kuma yadda yake anfani da kwayoyi. A ranar 25 ga watan yunin sheakarar 2009 Michael Jackson ya mutu, yayin da yake barci a wani gidan da yake haya a Holmby Hills da ke gundumar Los Angeles. Mutane da dama a fadin duniya sun yi ta jajanta mutuwar mawakin da ya shahara a wakoki irin na POP. 

Marigayi Michael Jackson
Marigayi Michael Jackson
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.