Isa ga babban shafi
MDD

MDD ta bayar da shawarar cin kwari a matsayin abinci

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bada shawarar cin kwari, a matsayin abinci ga dan Adam, domin kara habbaka abinci a duyniya, tare da kiwata su. Kwararu na hukumar ta abinci ta majalisar ta dinkin duniya, FAO sun bayyana cewa, cin kwarin da ake dasu a duniya karin ci gaba ne, wajen samarwa jiki nau’in abinci dake gina shi ga kuma dandano mai dadiHukumar ta FAO dai ta kafa hujja da cewa, cin kwari ga dan Adam ba bakon abu bane, domin kuwa a tsarin al’adun mutanen duniya, sama da biliyan 2 tun asalin ya gaji cin kwarin, don haka yana da kyau a ci gaba da cinsu, tare da kiwatasu.Eva Ursula Muller darakta ce a sashen da ke kula da siyasa, da kuma tattalin arzikin gandun daji, ta gabatar da wannan rahoto a birnin Roma na kasar Italiya, inda tace billiyoyin kwarin dake ci gaba da hayayyafa a doron kasa, da masu rayuwa a ruwa, dan adam na iya maidasu abinci, da kuma kiwatasu, wanda hakan zai takaita illar da suke yiwa mahalli a duk tsawon rayuwarsu,Binciken kwararun dai ya nuna cewa, akwai nau’ukan kwari sama da 900 da dan adam ka iya mayarwa cimakar a rayuwarsa, ga dadi ga kuma gina jiki, 

Kwaro abinci mai kyauy ne inji MDD
Kwaro abinci mai kyauy ne inji MDD DR
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.