Isa ga babban shafi
MDD-Afrika

Gonakkin yankin kasashen Afrika za su yi fama da kwari inji MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi kasashen Afrika da ke Arewa Maso Kudanci, da su yi hattara, domin akwai yiwuwar samun kwarin da za su mamaye gonakin yankin nan da makwanni masu zuwa.

Fara a saman ganyen itaciya
Fara a saman ganyen itaciya pestcemetery.com
Talla

Wannan gargadin ya fito ne daga Hukumar Kula da abinci da harkokin noma, ta Majlisar Dinkin Duniya, inda ta ke nuna cewa, wasu Fari sun doshi yankin kasashen Algeria da Libya da Mauritania da Morocco, kuma za su isa yankunan nan da makwanni masu zuwa.

Hukumar ta kwatanta cewa, dimbin Farin kan iya cinye abinci da mutane 35,000 za su ci a rana daya, wanda ya sa ta yi kira ga kasashen da su zamanto cikin shirin ko ta kwana.

Har ila yau, hukumar ta umurci kasashen da su tabbata sun saka wadanda za su saka ido dominsu fadakar da su akan zuwan farin, tare tanadar maganin kashe kwari.

Fari suna tafiya ne a kungiyance da yawansu kan kai Miliyoyi, kuma suna iya tafiyar kilo 150 a rana daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.