Isa ga babban shafi
Syria-Amurka

Amurka ta gargadi Hizbullah ta gaggauta ficewa daga Siriya

Amurka ta bukaci kungiyar Hizbullah da ke kasar Labanan, ta gaggauta janye dakarunta daga kasar Siriya inda suke taimakawa sojojin shugaba Bashar al-Assad a yakin da yake da ‘yan tawaye. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka Jen Psaki, ta bayyana rawar da kungiyar ta Hizbullah ke takawa a wannan yaki da cewa abu ne da Amurkar ba za ta lamunce ba.Wannan gargadi dai ya zo ne a daidai lokacin da ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius, ke cewa yanzu haka akwai dakarun kungiyar ta Hizbullah akalla dubu uku zuwa dubu hudu da suka shiga kasar ta Siriya domin kare gwamnatin Assad.Fabius, wanda ke gabatar da jawabi a gaban kwamitin harkokin wajen na karamar majalisar dokokin Faransa a jiya laraba, ya ce rawar da kungiyar ke takawa a wannan rikici abu ne da zai iya haifar da cikas ga kokarin da kasashen duniya ke yi wajen kawo karshen lamarin. 

Jagoran kungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah
Jagoran kungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah REUTERS/Manar TV via Reuters Tv
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.