Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Ana jiran rahoton Vatican kan zargin yin lalata da kananan yara

Wani kwamitin da ke kare hakkin yara a birnin Geneva ne ya fara wallafa bayanan inda ya nemi hukumomi a Fadar ta Vatican da ta yi bayani dalla dalla akan zargin cin zarafin kananan yaran ta hanyar yin lalata da su. 

Paparoma Francois
Paparoma Francois REUTERS/Alessandro Bianchi
Talla

Daga cikin bukatun da kwamitin ya mika shi ne yana son ya san irin matakan da Fadar ta Vatican ta dauka game da zargin, tare da sanin irin tallafin da aka bai wa wadanda aka ci zarafin nasu.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta nemi karin bayani akan batun musamman bisa zargin da ake yi na cewa ana jan kunnen wasu daga cikin yaran domin kin bayar da shaida dangane da abin da ya faru a kansu.

Paparoma Francis dai ya sha alwashin magance matsalar wacce tsohon Paparoma Bennedict na 16 ya taba bai wa wadanda aka ci zarafin na su hakuri.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil adama na ikrarin cewa Fadar ta Vatican na yin tafiyar hawainiya wajen magance matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.