Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka na fuskantar barazana

Manyan Jami’an gwamnatin Obama sun gudanar da wata ganawa ta musamman game da barazanar da Amurka ke fuskanta, lamarin da yasa gwamnatin kasar ta kudiri aniyar rufe ofisohin jekadancinta a kasashen musulmi a yau Lahadi.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Talla

Wadanda suka halarci zaman tattaunawar sun hada Susan Rice babbar mai bayar da shawara ga fannin tsaro da John Kerry sakataren harakokin waje da kuma Chuck Hagel sakataren tsaro.

An gudanar da zaman tattaunawar ne ba tare da shugaba Obama ba amma a cikin sanawar da ta fito manyar jami’an na gwamnatin shi sun ce umurni ne daga shugaban a dauki matakan kare Amurkawa saboda barazanar hare hare da ke fitowa daga kasashen Larabawa.

Akwai kuma gargadi daga hukumar tsaro ta Interpol a duniya game da barazanar tsaro da ke fitowa bayan ballewar manbobin Al Qaeda daga gidan yarin Pakistan.

Kasashen Jamus da Birtaniya da Faransa a yau Lahadi sun yi kira ga ‘yan kasashe su su kauracewa Yemen inda zasu rufe ofisoshin jekadancinsu a kasar na kwanaki biyu saboda baarazanar al Qaeda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.