Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka za ta bude ofisoshin jekadancinta a kasashen Larabawa

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce a gobe lahadi za a sake bude dukkanin ofisoshin jakancin kasar da aka rufe a wasu kasashen duniya da suka hada da na Larabawa da kuma arewacin Afrika Afirka amma ban da na birnin Sanaa da ke kasar Yemen saboda barazanar al Qaeda.

'Yan sanda suna aikin samar da tsaro a kan hanyar zuwa Ofishin jekadancin birtaniya a Sanaa kasar Yemen
'Yan sanda suna aikin samar da tsaro a kan hanyar zuwa Ofishin jekadancin birtaniya a Sanaa kasar Yemen REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ta Amurka Jen Psaki, ta bayyana cewa hatta ma karamin ofishin jakadancin kasar da ke birnin Lahore da ke kasar Pakistan zai ci gaba da kasancewa a rufe.

Amurka ta dauki matakin rufe ofishoshinta a cikin kasashe 25 makon da ya gabata sakamakon abin da ta kira babbar barazana daga kungiyar Al Qaeda.

Gwamnatin Yemen ta yi ikirarin samun nasarar warware wani hari da kungiyar al Qaeda ta kulla kai wa a wani kamfani hako mai na kasashen waje, a dai dai lokacin da barazanar kungiyar ke razana Amurka da kasashen Turai.

Kakakin gwamnatin Yemen Rajeh Badi ya shaidawa kamfanin dullacin labaran Faransa cewa an shirya kai harin ne a wani kamfanin kasar Canada, Tare da yukurin yin garkuwa da ma’akaitan kamfanin.

Tuni dai Amurka da Birtaniya suka rufe ofisoshin jekadancinsu a birnin Sanaa saboda barazanar da suka ce sun samu ta kaddamar da hare hare daga kungiyar al Qaeda reshen Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.