Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

Za a fara tattaunawa tsakanin Isra’ila da Falasdinawa

Yau ne ake sa ran Isra’ila da Falasdinu za su fara tattaunawar keke da keke, a wani sabon yunkuri na sasanta rikicin Gabas ta tsakiya, da kuma fatar ganin an samu kasar Falasdinu.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu (Hagu) Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas (Dama)
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu (Hagu) Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas (Dama) Reuters/Montage RFI
Talla

Sai dai taron ya gamu da cikas, sakamakon kaddamar da gina wasu sabbin gidaje kusan 1,000 a Yankunan Falasdinawan, amma Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya ce shugaba Mahmud Abbas a shirye yake ya cigaba da tattaunawa da Isra’ila duk da matsalar dake tsakanin su.

Koda yake kasar ta Isra’ila ta saki wasu Falasdinawa 26 da take tsare da su a gidajen yarin ta, kafin fara taron da ake sa rai za a yau tsakanin bangarorin biyu.

Da asubahin yau, motocin dake dauke da Falasdinawan ta tsallaka Gaza daga gidan yarin tsakiyar birnin kudus, inda daruruwan mutane suka tarbe su, cikin su harda shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.