Isa ga babban shafi
Amurka

Bukin Tuna Martin Luther King a Amurka

A yau Laraba ake gudanar da bukukuwan cika shekaru 50 da jawabin da bakar fata dan gwagwarmaya a kasar Amurka Martin Luter King ya gabatar, inda a cikin ya ke cewa ya yi mafarkin za a wayi gari a samu daidaito tsakanin bakake da farare a kasar Amurka.

Martin Luther King yana jawabin Na yi Mafarki a Amurka
Martin Luther King yana jawabin Na yi Mafarki a Amurka Library of congress
Talla

“Na yi mafarki” (I Have Dream) shi ne jawabin Martin Luther King wanda ya yada fatawar yaki da wariyar launi fata a kasar Amurka.

Wannan jawabin tarihi ne da ya shafi Barack Obama wanda shi ne shugaba bakar fata na farko a Amurka, kuma hakan ya tabbatar da nasarar Luther King na kawo karshen wariya a kasar.

Martin Luther King, yace ya yi mafarki wata rana za’a wayi gari bayi da ‘yayansu zasu hada kai domin dunkulewa waje daya a Amurka

A tarihin Amurka wannan Jawabin na luther king, yana cikin jerin jawabai da ke sosa ran Amurkawa, a wani gangami da Martin Luther king ya hada a birnin Washington.

A shekarar 1968 ne aka kashe Martin Luther king amma yanzu bayan gushewarsa an samu shugaba bakar fata a Amurka kuma bayan mutuwarsa akwai Kofi Annan, Sakataren majalisar Dinkin Duniya da aka samu bakar fata, duk da babbar rawa da Amurka ke taka wa a zauren Majalisar.

Sanadiyar fafutukar Matin Luther king ne, a shekarar 1964 aka kafa dokar yaki da wariya a Amurka.

Shugaban Amurka Barak Obama ne zai jagoranci Amurkawa domin tuna Martin Luter King.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.