Isa ga babban shafi
Amurka-Syria

Obama ya daura wa Assad laifin kai harin Makamai masu guba

Shugaban Amurka Barack Obama yace sun tabbatar da dakarun Assad sun yi amfani da makamai masu guba amma shugaban ya jinkirta bayar da umurnin kai wa kasar hari, amma komi na iya faruwa saboda yace amfani da makamai masu guba ketare iyaka ne, kuma Gwamnatin Syria ce ke da alhaki.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Jason Reed
Talla

Duk da cewa Birtaniya ce ta gabatar da kudirin kai wa Syria hari a kwamitin Sulhu amma sabanin ra’ayi daga bangeren masu adawa da matakin a kasar na cusa shakku ko Amurka za ta samu goyon bayan Birtaniya wajen kaddamar da yaki a Syria.

Akwai kuma adawa da sabanin ra’ayi da Kasar Amurka ke fuskanta daga Rasha na hana kwamitin sulhu a Majalisar Dinkin Duniya daukar duk wani mataki na hukunta kasar Syria, kan amfani da makami mai guba a cikin kasar.

Mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron Amurka, Marie Harf, tace an kasa samun ci gaba a yunkurin Amurka da Birtaniya da Faransa ke yi na ganin an dauki mataki kan Gwamnatin shugaba Bashar al Assad.

Jami’ar tace, ba zasu ci gaba da lallashin Russia ba a zauren Majalisar Dinkin Duniya, saboda matakin na Syria na bukatar gaggawa.

Yanzu haka wakilan Majalisar Dinin Duniya suna cikin kasar Syria domin gudanar da binciken sahihin wanda ke da alhakin kai harin makami mai guba a cikin kasar.

Sakatare Janar na Mjalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, ya bukaci ganin an bai wa jami’an da ke gudanar da bincike a Syria damar gudanar da ayyukan su.

Yayin da ya ke jawabi, Ban ya koka kan riga malam masallaci da wasu kasashe ke shirin yi.

A wata ganawa ta wayar Salula da shugabannin kasashen Iran da Rasha suka yi aminan Bashar al Assad, Vladimir Putin da Hassan Rouhani sun la’anci hare haren da aka kai na makamai masu guba a Syria amma sun bayyana adawarsu da duk wani yunkuri na abkawa kasar.

Obama yace Amurka a shirye ta ke ta kaddamar da yaki a Syria amma suna jiran lokaci ne saboda shiga yaki bayan mutuwar mutane sama da 100,000 ba zai zama hanyar dogaro ba.

Obama yana kokarin kawo karshen yake yaken da Amurka ke shiga a kasashen duniya amma yace keta dokokin duniya al’amari ne da ke bukatar kulawar gaggawa.

Amurka da Birtaniya da Faransa suna neman shiga Syria ne kamar yadda suka abka wa Kanal Gaddafi na Libya duk da adawar China da Rasha a zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Amma akwai baraka da David Cameron ke fuskanta ta sabanin ra’ayi daga Majalisar Birtaniya akan Syria wadanda wasu daga cikinsu suka bukaci Firaministan ya jinkirta daukar matakin Soji har sai wakilan Majalisar Dinkin Duniya sun tabbatar da gaskiyar wanda ke da alhakin yin amfani da makamai masu guba a Syria.

Majalisar Dinkin Duniya tace wakilanta suna bukatar lokaci domin kammala bincikensu a kasar Syria.

‘Yan tawayen Syria sun ce mutane 1,300 ne suka mutu a Syria sakamakon hare haren makamai masu guba. Amma Gwamnatin Assad ta karyata zargin da ake mata, yayin da take zargin ‘Yan tawayen.

Mai shiga tsakanin rikicin Syria na Majalisar Dinkin Duniya Lakhdar Brahimi, ya yi gargadin cewa daukar matakin Soji akan Syria mataki ne da zai tarwatsa yankin Gabas ta tsakiya.

Dubban mutanen ne dai suka fice daga Syria domin tsira da ransu, yayin da alkalumman Majalisar Dinkin Duniya suka ce mutane sama da 100,000 ne suka mutu tun fara rikicin kasar a watan Maris din 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.