Isa ga babban shafi
Amurka-Iran-Isra'ila

Za mu iya ya hana Iran mallakar makamin nukiliya mu kadai- Netanyahu

Firaministan Isra’ila Benjamin Natanyahu ya ce suna iya yaki da Iran akan haramta mata mallakar makaman Nukiliya tare da kira ga kasashen duniya da su nisanta kansu daga kulla kawance da sabuwar gwamnatin Hassan Rohani.

Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu Reuters
Talla

Natanyahu wanda ya soki shirin Iran na Mallakar makaman nukiliya a zauren Majalisar Dinkin Duniya ya ce suna iya zama da kafarsu domin ci gaba da adawa da Iran.

"Ba za mu bar Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, idan ya zama dole mu tsaya mu kadai domin yin adawa da Iran, za mu yi hakan." Inji Netanyahu.

A cikin jawabin na Natanyahu, Firaminsitan na Isra’ila ya mayar wa Rohani da martani, wanda ya ce sabon shugaban na Iran ya na neman ya yaudari duniya ne ta hanyar lallashi.

Kuma Natanyahu ya yi kiran a karfafawa Iran takunkumi tare da jaddada cewa ta na dab da mallakar makaman na Nukiliya.

Ko a shekarar da ta gabata a wani jawabi da Firaministan ya yi a gaban zauren Majalisar, ya yi amfani da wani zane dake nuna cewa Iran din na dab da mallakar makamin na nukiliya, inda ya yi kira ga kasashen duniya ta su dauki matakin gaggawa domin dakile shirin.

To sai dai tawagar Iran a zauren na Majalisar Dinkin Duniya sun mayar wa Natanyahu da martani suna masu sheda masa cewa a shirye suke su kare kansu ga duk wani harin Isra’ila.

Tun kafin jawabin na Netanyahu ne Ministan harakokin wajen Iran ya danganta jawaban shi a matsayin shaci fadi.
Irin wannan sabanin da ake samu tsakanin Isra’ila da Iran, shi ke haifar da rashin jituwa tsakanin kasashen duniya akan Iran.

Sabon shuagban kasar kasar Iran Rohani a ‘yan kwanakin nan ya bayyana shirin kasar Iran na hawa teburin tattaunawa da kasashen Yammacin duniya domin ya bayyana asalin niyyar kasar ta Iran game da shirin nata.

Tuni wannan ta yi na Rohani har ya haifar da wata ganawa da shugaban ya yi na takwaransa na Amurka Barack Obama ta wayar talho inda suka tattauna game da shirin nukiliyar na Iran.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.