Isa ga babban shafi
Syria

Lakhadar Brahimi ya kai ziyara kasar Syria

A yau Litinin manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar hadin kan larabawa Lakhdar Brahimi, ya isa kasar syria, inda zai nemi hadin kan bangarorin da ke rikici da juna a kasar, wajen gudanar da taron samar da zaman lafiya na Geneva a kasar Switzerland.

Lakhdar Brahimi yayin da yake amsa maraba a lokacin da ya isa kasar Syria
Lakhdar Brahimi yayin da yake amsa maraba a lokacin da ya isa kasar Syria REUTERS/Khaled al-Hariri
Talla

Brahimi, ya isa birnin Damascus ta hanyar mota, bayan zuwa kasar Lebanon a jirgin sama, daga Iran, ya kuma je kasar Turkiya, sai dai bai je Saudi Arabiya ba.

Dama hukumomin na birnin Riyadh sun sa kafa sun yi fatali da shirin taron, inda suka ci gaba da nuna adawa da shugaba Bashar al-Assad.

A birnin Tehran, Brahimi ya ce kamata ya yi Iran, da ke matsayin aminiyar kasar ta Syria, ta shiga a dama da ita a taron na birnin Geneva, da za a yi wata mai zuwa, da kuma ake fatan ya taimaka wa jen kawo karshen yakin basasan da aka fiye da watanni 30 ana gwabzawa.

Mista Brahimi na fatan amfani da ziyarar, don neman hadin kan gwamnatin, da ‘yan tawayen su shiga a dama da su a taron na Geneva.

A halin da ake ciki kuma kasar Rasha ta yi Allah wadai da barazanar da ‘yan tawayen Syria suka yi wa masu shirin halartar taron zamana lafiyan, inda suka ce za su kama su da laifin cin amanar kasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.