Isa ga babban shafi
Amurka

Za’a datse kasafin kudin tsaron Amurka

Wani Babban Kwamandan Sojin Amurka ya yi gargadin samun matsala idan har Majalisa ta datse kasafin kudin Sojin kasar wanda ya ke ganin hakan zai haifar da baraka ga Sojojin idan har suna fagen yaki saboda rashin samun horo.

Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel
Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel REUTERS/Kevin Lamarque/Files
Talla

Janar James Amos wanda shi ne babban kwamandan Sojin Amurka ya yi gargadin cewa datse kasafin kudin zai haifar da matsaloli ga bangaren Sojin kasar, yana mai la’akari da cewa hakan zai shafi karancin horo da Sojin Amurka zasu samu anan gaba.

A cewar Janar Amos, rashin samun horo na Sojin Amurka babbar baraka ce da zai iya haifar da tsaiku a duk lokacin da Amurka ke shirin abkawa yaki.

Kalaman Janar din na Sojan Amurka sun yi dai dai da kalaman Sakataren tsaron kasar Chuck Hagel wanda tun a farko ya yi gargadin dole sai an rage yawan dakarun Amurka domin daidaita kasafin kudin kasar a badi.

Mista Hagel yace kudirin datse kasafin kudin, mataki ne da majalisar Amurka ke shirin dauka a gaggauce.

Shugabannin Sojin kasar sun nemi Majalisar Amurka ta sassauta domin hakan zai haifar wa dakarun kasar Matsala a fagen yaki saboda wasu da za’a sallama.

Yana mai gargadin karancin soji a fagen yaki barazana ce ga Amurka saboda zai kai ga har sai an kammala yaki kafin dakarun su fice daga fagen yakin.

Kudaden da ake shirin zabge wa bangaren tsaron na Amurka, adadin zai zarce na bara kusan kashi 10 daga kasafin kudin bangaren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.