Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

MDD ta bukaci Fadar Vatican ta mika masu yin lalata da Yara ga ‘Yan sanda

Hukumar kare kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci fadar Vatican ta Fafaroma ta tube Malaman Darikar Katolika daga mukaminsu wadanda ake tuhuma da yin lalata da kananan yara tare da mika su ga ‘Yan sanda.

Fafaroma François,Shugaban Darikar Katolika a Fadar Vatican da ke kasar Italiya a lokacin da ya ke jawabi ga dubban mabiya
Fafaroma François,Shugaban Darikar Katolika a Fadar Vatican da ke kasar Italiya a lokacin da ya ke jawabi ga dubban mabiya REUTERS/Osservatore Romano
Talla

Kwamitin da aka nada domin gudanar da bincike akan matsalar ya yi suka ga sabbin tsare tsaren da Fadar Vatican ke aiwatarwa domin ba masu yin lalata da kananan yara damar ci gaba da gudunar da mummunar tabi’ar ta lalata rayuwar dubban kananan yara.

Hukumar ta kuma zargi Fadar Vatican akan yadda take tunkarar mu’amular jinsi da zubar da ciki.

Akwai kwamiti da Fadar Vatican ta kafa domin yaki da matsalar lalata da kananan yara a darikar Katolika kuma ana sa ran zasu fitar da sanarwa akan rahoton.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa akan yadda fadar Vatican ke jan kafa wajen yaki da matsalar cin zarafin kananan yara musamman tsakanin manyan Limaman darikar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.