Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

MDD ta zargi Vatican da kin mika bayanan cin zarafin bil adama da aka aikata a fadar

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Fadar Paparoma dake Vatican ta ki bata bayanan cin zarafin yara kanana da ake zargin fada fada mabiya darikar Katolika da aikatawa.

Paparoma Francis
Paparoma Francis REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Ita dai Fadar ta ce kasashen da aka aikata laifufukan ne kawai ke da hurumin hukunta fada fadan da ake zargi, ba Majalisar Dinkin Duniya.

Wannab kuma na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara tuhumar wani babban limamin fadar Nunzio Scarano akan zargin danne wasu kudade da ya yi.

Yanzu haka an dage sauraren karar zuwa ranar 13 ga watan Dismba inda za a saurari bahasin shaidan farko.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.