Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Paparoma Francis ya cire wani babban jami’in Fadar Vatican daga mukaminshi

Paparoma Francis ya tsige Sakataren harkokin kasashe na Fadar Vatican a yunkurin da yake yin a ganin an tsabtace fadar daga baragurbin dake kawo matsaloli a fadar.

Paparoma Francis a lokacin ziyararsa a Brazil
Paparoma Francis a lokacin ziyararsa a Brazil REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

An cire Tarcisco Bertone daga mukaminshi inda aka maye gurbinshi da Pietro Parolin wanda a da yake rike da wani matsayi a kasar Venezuela.

Dan shekaru 58, wasu da daman a kallon Parolin a matsayin sabon jinni da zai iya taimakawa wajen tabbatar da biyan bukatun Fadar ta Vatican.

‘Ina sane da wannan babban nauyi da aka dora min, wannan kuma babban kalubale ne a gare ni dake nufin na tashi na yi aiki tukuru.” Inji Parolin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.