Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Fadar Vatican ta mayar da martani game da lalata da Yara

Fadar Vatican ta mabiya darikar Katolika a duniya, ta zargi Majalisar Dinkin Duniya da nuna son-rai a cikin rahotonta da ke zargin ba a daukar batun yin lalata da kananan yara da ake zargin wasu fada-fadanta da aikatawa da muhimmanci. Babban sakataren Vatican Pietro Parolin, yace suna shirin daukar mataki kan Majalisar Dinkin Duniya dangane da wannan zargi.

Fadar Vatican a birnin Rome
Fadar Vatican a birnin Rome Reuters/Alessandro Bianchi
Talla

Fadar Vatican ta mayar da martani mai zafi da cewar hukumar kare hakin bil’adama na kaucewa gaskiya sakamakon rashin ganin sabbin matakan da Fadar Vatican ke dauka na ganin ta magance wannan matsalar da ta addabi darikar Katolika.

Wannan sa-in-sa din dai ya biyo bayan rahoton da majalisar Dinkin Duniya ta fitar da ke cewa kwamitin kare hakkin kananan yara ya zargi fadar da kasa tsabtace ayyukan malamanta daga badakalar cin zarafin kananan yara da ta dau alkawarin yi sau da dama a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.