Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine-Amurka

Obama da Putin sun gana ta wayar talho kan kasar Ukraine

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin ta wayar talho sa’o’i kadan bayan da Amurkan ta haramta baiwa jami’an Rasha takurdun iznin shiga kasar ta. 

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Rahotanni sun ce shugabanni biyu sun kwashe akalla sa’a guda suna tattaunawa inda Obama ya jaddadawa Putin cewa matakain da Rasha ta dauka kan Ukraine na mamaye Crimea ya keta hakkin Ukraine a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta.

Ganawar da shugabannin biyu suka yi na zuwa ne yayin da hukumomi a birnin Kiev suka sanar da rusa majalisar dokokin lardin Crimea wadda a jiya ta amince mazauna lardin su jefa kuri’ar bai wa yankin damar hadewa da kasar Rasha a ranar 16 ga wannan wata na Maris.

Sabuwar gwamantin kasar ta Ukraine mai ra’ayin kulla alaka da kasashen Turai, da kuma sauran kasashen yammacin duniya da dama ne suka bayyana wannan yunkuri a matsayin wanda ya sabawa doka.

Yayin da ake wannan takaddama yanzu haka hukumomi a kasar ta Ukraine har ila yau sun bukaci hukumar ‘yan sandar kasa da kasa wato Interpol, da ta gaggauta fitar da sammacin kama hambararren shugaban kasar mai samun goyon bayan Rasha Viktor Yanukovych domin gurfanar da shi a gaban kuliya sannan a tuhume shi da laifin zubar da jinin al’ummar kasar.

A taron da suka gudanar jiya alhamis a birnin Brussels, ministocin harkokin wajen kasashen Turai, sun gargadi Rasha da ta kawo karshen shisshigin da take yi a al’amurran cikin gidan kasar ta Ukraine, tare da furta barazanar sanyawa kasar takunkumai.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.